Rukayya Dawayya |
A cikin 'yan kwanakin nan ne rahotanni suka bayyana cewa aure fitacciyar jarumar finafinan Hausan nan, Rukayya Umar Santa, wadda aka fi sani da Rukayya Dawayya ya mutu.
Majiyarmu ba ta tabbatar da ranar da auren ya mutu ba, amma wata majiya mai tushe ta tabbatar da mutuwar auren jarumar da mijin nata, Alhaji Adamu Mohammde Teku, wanda dan asalin garin Yola ne da ke jihar Adamawa, amma mazaunin babban birinin tarayya Abuja ne.
A hirar da jarumar ta yi da mujallar Fim game da batun mutuwar auren nata, Dawayya ta tabbatar da hakan, inda ta kara da cewa "Allah ya hada ni da wani irin miji wanda shi sakin mace a gurin sa ba komai ba ne. Domin akalla ya saki mata sun fi goma sha biyar. To, ka ga kuwa don ni ya sake ni ba zai zama wani abu ba".
Kafin rabuwar Dawayya da mijin nata, Allah ya azurta su da da namiji, wanda aka sanya masa suna Arfat, bayan ta haife shi a kasa mai tsarki a yayin da ta je aikin Hajji a shekarar da ta gabata.
Bikin wanda Dawayya, wanda ka yi shi kusan shekaru biyu da suka gabata, yana daya daga cikin kayatattun bukukuwan auren da aka yi a tarihin masana'antar fim, kasancewar irin wadakar da aka yi da dalolin kudi a yayin shagulgulan bikin, ganin cewa mijin dan siyasa ne, wanda aka dauki tsawon kwanki hudu ana yi.
Sannan kuma bikin ya kafa wani tarihi a msana'antar fim, domin a yayin da za a rako amaryar zuwa gidan mijinta da ke Abuja, a jirgi a ka kawo ta tare da ita da kawayenta, inda bayan an zo Abuja ma, aka sake cashewa da wani sabon shagalin biki.
Auren wanda aka biya sadaki naira dubu hamsin, majiyarmu ta bayyana cewa Dawayya ta hadu da mijin nata ne a Abuja, a yayin da take kan daukar wani fim dinta mai suna A'isha, inda ba da jimawa ba bayan sun fahimci junansu sai kawai aka sanya ranar aure.
SOURCE: RARIYA
No comments:
Post a Comment